1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta jaddada manufofi kan bakin haure

Suleiman Babayo
August 14, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatar da matsayi kan kare bakin haure masu neman shiga kasashen Turai bisa dalilai nan tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/33ATs
Deutschland Bundeskanzlerin Merkel stellt sich Fragen der Bürger in Jena
Hoto: Reuters/F. Bensch

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kare manufofin gwamnatin kasar kan bakin haure masu neman zuwa kasashen Turai. Misali shi ne aikin hadin gwiwa da gwamnatin Jamhuriyar Nijar da sauran kasashen Turai kamar Jamus da Italiya da Faransa gami da kungiyar Tarayyar Turai domin dakile hanyoyin da bakin haure ke bi domin kai wa ga kasashen Turai.

Angela Merkel ta yi karin hasken a garin Jena na gabashin kasar ta Jamus. Hakan na zuwa ne yayin da za ta karbi bakuncin Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar a birnin Berlin fadar gwamnati domin ci gaba da tattauna batun na Afirka.