1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gauck: "Deutschland darf sich nicht verstecken"

Usman ShehuFebruary 23, 2014

Shugaban ƙasar Jamus Joachim Gauck ya bayyana mahimmanci dalilan da suka sa ƙasar a ya waja ba kanta na yin hoɓɓasa kan al'amuran da ke faruwa a duniya.

https://p.dw.com/p/1BE8e
Joachim Gauck Dritte Generation Ostdeutschland 14.11.2013 in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayin da shugabannin duniya ke ci-gaba da tofa albarkacin bakinsu kan dabbaruwar siyasa da ke faruwa a ƙasar Yukren, tashar DW ta yi hira da shugaban ƙasar Jamus Joachim Gauck, wanda ya ce a matsayin ƙasar Jamus na mai faɗa aji a nahiyar Turai, ba za ta rufe idanunta tana ganin abin da ke faruwa a Yukren ba.

Shugaban ƙasar Jamus dai, ya fara ne da tuna baya, inda ya bayyana cewa ƙasar Jamus bisa tarihi ƙasa ce da ta san irin illolin da yaƙi ke kawowa, kuma dole a irin yanayin da Yukren ta shiga Jamus ta sa baki. Don haka ya ce tare da haɗin gwiwar sauran ƙasashen Turai, Tarayyar Jamus za da gudumawa da ta kamata.

"Ba dai-dai ba ne gare mu, a ce mun gyale abin da ke faruwa, abin da yake faruwa a bayan gidanmu, wato kan iyakar makobciyarmu ƙasar Poland. A wannan ƙasar al'ummar ta tuni sun daɗe cikin ƙasashen Turai, musamman wani ɓangaren ƙasar ta Yukren, kai har ma ƙasar baki ɗayanta. Kazalika a ƙasar akwai alaƙar al'adu matuƙa, kuma mutanen ƙasar sun dogara ne da ƙasashen Yamma fiye da yadda suke alaƙa da Moscow".

Gauck DW Interview 21.02.2014
Hoto: Bundespresseamt/Jesco Denzel

Shugaban ƙasar ta Jamus a hirar tasa da DW ya bayyana cewa, wannan matsayin na ƙasar Jamus a harokin ƙasashen waje, ya kasance wani babban abin da har cikin gida 'yan ƙasar ci gaba da yin alhara da shi, domin ganin Jamus ta yi hobbasa a wani abin da ke faruwa wata ƙasa. Kuma a zahiri bai kamata ƙasa ta kasance babbar banza ba.

"A ciki da wajen ƙasar ana ɗaukar rawar da muke takawa da mahimmanci, kuma 'yan ƙasarmu na gamsuwa da haka. Domin ina jin sun fahimci haka bisa al'adu da maƙobtanmu. Domin a da ba mu cika sa baki kan al'amuran wasu ƙasashe ba, sabo da irin tabon da muke da shi bisa tarihin ƙasar mu. Kuma wannan shi ne tunanin aksarin jama'armu"

Joachim Gauck ya kuma ba da dalilan da suka sa ƙasashen duniya ba za su rufe idanunsu, suna ganin abin da ke faruwa a ƙasar Yukrain ya ci ga ba, inda tuni aka fara samun asaran rayuka, bisa arangama da ake yi tsakanin jami'an tsaro da masu adawa da gwamnati. Shugaba Gauck, ya ambaci wasu ƙasashen da aka samu rikicin siyasa a baya, kuma ya haifar da kisan kiyashi kan jama'a. Don haka yace rashin ɗaukar mataki mai ƙarfi, yakan kasance muguwar dabara.

Ukraine Krise Trauer um Opfer 22.02.2014
Hoto: Reuters

"A nan Turai muna tuna abin da ya faru Srebrenica, hakan ya nuna wasu lokutan zance na baka kawai baya iya kawo sauyi. Ka zalika mun ga abin da ya faru a ƙasar Ruwanda, munga abin da ya faru idan ba'a yi amfani da ƙarfi wajen magance rikicin siyasa cikin gaggawa ba. Don haka akwai bambanci tsakanin ƙarama da kuma babbar matsala, wajen warware wani rikici"

A ci gaba da nuna irin matsayin Jamus tsakanin ƙasashen Turai, a watan Maris shugaba Joachim Gauck zai ziyarci ƙasar Girka, inda can zai jaddada matsayin Jamus na tabbatar da ƙasar ta Girka ta sake tsayawa kan ƙafafunta, bayan rikicin siyasa da na tattalin arziki da ta fiskanta. Sai dai shugaban na ƙasar Jamus ya kuma yi suka kan Jamusawa, inda ya ce har yanzu, wasu 'yan ƙasar ta Jamus ba su saki jiki da baƙi 'yan ci rani ba. Lamarin da ya ce wannan yana nuna cewa har yanzu Jamus ba ta kai ga zama mai cikakken demokraɗiyaya ɗari bisa ɗari ba.

Mawallafa: Naomi Conrad /Usman Shehu Usman Edita: Abdourrahman Hassane