1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Ci gaba da fitar da abinci

March 18, 2023

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cimma matsaya kan sabunta yerjejeniyar fitar da kayan abinci daga Ukraine ta Tekun Bahar Aswad.

https://p.dw.com/p/4OtHj
Istanbul  | Ukraine | Abinci
Cimma yarjejeniya kan ci gaba da fitar da abinci daga UkraineHoto: Khalil Hamra/AP/picture alliance

Erdogan ya sanar da hankan ne a ranar Asabar 18.03.2023 yayin wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, inda ya ce bayan tattaunawa da bangarorin biyu dukanninsu sun yi na'am da tsawaita yerjeniyar sai dai bai yi karin haske kan tsawon wa'adin da za ta kwashe ba.

Sabuwar yerjeniyar za ta fara aiki ne daga gobe Lahadi 19 ga watan Maris a cewar fadar Ankara, sai dai har kawo yanzu ana jayayya da fadar Kremlin kan batun wa'adin da za ta kwashe. Yayin da Turkiyya ke fatan ganin an tsawaita yarjejeniyar da kwanaki 120, Rasha kuwa na ci gaba da dagewa kan rage wa'adinta zuwa kwanaki 60 kacal.

Ana dai kyautata fatan sabuwar yerjejeniyar idan har kasashen biyu sun mutumta ta, za ta kawo sauki ga fargabar karancin abinci a duniya sakamakon yakin Rasha da Ukraine.