1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Yanayin aiki a Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe SB/LMJ
March 14, 2023

Jamus na ci gaba da zawarcin kwararrun ma'aikata 400,000 a kowace shekara don cike gibin da take da shi a fannin kwadago sakamakon tsufar al'umma. Galibin ma'aikatan da ke shigowa Jamus daga ketare suna sake ficewa.

https://p.dw.com/p/4OeMP
Jamus I hukumar kodago ta Jamus
Hukumar kwadago ta JamusHoto: Peter Hille/DW

A lokacin da Mara da ke zama ‘yar asalin Romaniya ta sami aikin da ake biyan albashi mai tsoka a masana'antar talla a birnin Berlin, wani bangare na burinta ne ya cika. 'Yar shekaru 30 da haihuwar ta yi karatu a Biritaniya, kuma ta yi aiki a Romaniya na 'yan shekaru kafin ta yi hijira zuwa Jamus domin fara sabon aiki. Sai dai murnarta ta fara kowama ciki kankanin lokaci, inda ta fara fuskantar kadaici sakamakon rashin aboki ko kawa da za su iya cire mata kewa. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da rashin nakaltar harshen Jamusanci, duk da cewa ta yi takaitaccen kwas din Jamusanci a birnin Bucharest.

Ba Mara kadai ce bakuwa da take fuskantar matsallin sajewa a Jamus ba. Cibiyar nazarin tattalin arziki ta Tübingen da hukumar samar da aikin yi ta Jamus sun binciki kusan ma'aikata 'yan kasashen waje 1,900 ta hanyar Facebook, inda suka yi korafe-korafe game da rashin rashin kyakyawar ma'amala tsakanin baki da 'yan kasa. Kashi biyu bisa uku na kwararrun ma'aikata da suke da tushe da kasashe  Turai sun bayyana cewa sun fuskanci wariya a Jamus saboda asalinsu. Sannan Malama Mara ta ce takardar izini zama a Jamus yana da matsala musamman ga baki da ba su fito daga kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ba.

Cibiyar hukumar kwadago ta Jamus mai kula da baki
Cibiyar hukumar kwadago ta Jamus mai kula da bakiHoto: Zoonar/picture alliance

Wannan juya wa Jamus baya da kwararrun ma'aikatan ketare ke yi na mummunan tasiri a fannin kwadago. Ko da mai binciken a Berlin kan kaurar al'umma Naika Fourutan, wacce ke koyarwa a jami'ar Humboldt, sai da ta ce kididdiga ta nunar da cewa kwararrun ma'aikata 'yan kasashen waje na saurin ficewa daga kasar. Hasali ma Jamus ta samu koma baya a fannin tagomashi a fannin kwadagro. A yanzu haka tana a matsayi na 15 daga cikin kasashe 38 na OECD da ke albashi mai tsoka da makoma ta gari da ba da dama ga iyalan ma'aikata da ingancin rayuwa. A cewar hukumar kwadago ta Jamus, dole ne a samar da kwararrun ma'aikata 400,000 a kowace shekara don ci gaba a kasuwar kwadago. Amma dai ma'aikata 40,000 ne kawai suka shiga kasar a 2021.

A halin yanzu dai gwamnatin tarayya tana kokarin yin garambawul ga dokar shige da fice, don saukaka wa wadanda suka shekara biyar zama 'yan Jamus. Amma kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewar kashi 59 cikin 100 na Jamusawa sun ki amincewa da ba da izinin zama dan kasa cikin sauri. Amma wannan matsayi zai iya jefa Jamus cikin mummunan hali, saboda Birtaniya da Amirka da Kanada da Ostiraliya sun yi nisa wajen jawo kwararrun ma'aikata a jika ta hanyar sawwaka musu yin hijira da samun aiki.