Matatun mai a Najeriya za su fara aiki | Labarai | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matatun mai a Najeriya za su fara aiki

Hukumar kula da man fetir ta kasar Najeriya NNPC ta sanar cewa, matatun mai na kasar guda hudu da ke tsaye yau shekaru biyu, za su fara aiki a watan Yuli.

Kakakin hukumar ta NNPC Ohi Alegbe, ya yi wadannan kalammai ne a daidai lokacin da kasar ta Najeriya wadda ta fi ko wace kasa arzikin man fetur a Afirka, ke fama da matsalar karancin na mai. Ya ce matatun mai na Warri, da na Port Harcourt da ke kudancin kasar, da kuma matatar mai ta Kaduna da ke arewa duk za su soma aiki a cikin wata mai zuwa na Yuli. A watan da ya gabata ma dai an fuskanci babbar matsalar karancin man fetir din a Najeriya, bayan da manyan 'yan kasuwar mai na kasar suka bukaci a biyasu bashin kudadan tallafin da ya kai kimanin Euro miliyan 900.