1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matakin kotun Jamus kan motoci masu amfani da man-dizal

Usman Shehu Usman
February 28, 2018

Daga yanzu dai wasu garuruwan kasar Jamus kan iya haramta motocin da ke amfani da man-dizal shiga biranen musamman masu fitar da hayaki mai gurbata mahalli.

https://p.dw.com/p/2tSlJ
Deutschland Fahrverbort in Städten
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Meissner

Yanzu tambayar ita ce wai shin garuruwan za su fara aiwatar da dokar ko kuma za su jira har sai daukacin jihohin kasar sun dauki tsarin a matsayin doka. Wannan na cikin muhawarar da ake ta yi, tun bayan da kotu ta yanke hukunci bisa kara da wasu biranen Jamus suka shigar kuma aka ba su nasara.

Schild Feinstaub Fahrverbot
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Dedert

 

Hukun dai ba ga kasar Jamus kawai zai shafa ba, amma har da sauran kasashen Turai, domin in an fara aiwatar da dokar to dole daga kan iyakar kasar Jamus za a  fara aiwatar da ita, inda yanzu yanzu motocin kasashen Turai kan shigo Jamus ba tare da wani ya tambayesu, kasancewa babu shingayen kan iyaka. Tuni ma dai ita kanta gwamnatin Jamus ta yi na'am da wannan hukuncin. Inda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a martaninta kan hukuncin.

Symbolbild Diesel-Fahrverbot in Städten
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Yanzu dai abun da rage shi ne hukumar da za ta tabbatar aiko da wannan dokar domin tuni 'yan sandan kasar ta Jamus suka ce basu da isassun ma'aikata da za su iya kula da motoci dauke da hayaki mai gurbata mahalli haka kuma suma sauran jami'an kula da da'a na biranen sun ce aikin ya fi karfinsu, yanzu abin da ya saura shi ne, masanan za su duba yadda za saka na'urorin kamara da za su rika kula da masu karya dokar. Sai dai a kasa kamar Jamus da mutane ke da 'yancin mai yawa, wasu na gudun cewa saka na'urorin da za su dauki hotunan a matsayin keta 'yancinsu. Saboda haka da sauran mahawara kafin sanin yadda doka haramta motocin masu amfani da man-dizal da ke gurbata mahalli a kasar ta Jamus.