Matakan sasantawa tsakanin Jamus da Poland | Labarai | DW | 11.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan sasantawa tsakanin Jamus da Poland

An fara daukar matakan da za su yafa ruwa bisa tsamin dangantakar Warsaw da Berlin bayan kalaman da wasu 'yan siyasar Jamus suka yi kan sauye-sauyen tsarin shari'ar makobciyar tasu.

A yayin da suke wata tattaunawa tsakanin su a ranar litinin din nan da Jamus ministan harkokin wajen Poland Witold Waszczykowski ya ce basu da tsamin dangantaka da tarayyar Jamus .

Itama tarayyar Jamus a nata banagaren ata bakin Steffen Seibert cewa yake.

Jamus na matikar son cigaba da wanzar da danganta ta kut da kut a yayin da wannan tattaunawar ita ce wadda muka mayar da hankalin mu a kai, don yanke hukunci yana rataye a wuyan shugabar gwmnatin Jamus ce da Firiministan Poland wajen kara yaukaka dangantaka.

Dangantaka tsakanin Jamus da Poland dai tayi tsamine tun lokacin da jami'iyyar PIS ta sake komawa gadon mulkin kasar a watan Oktoba bayan ta shafe shekaru takwas a matsayin jam'iyyar adawa.