1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Jamus: Kokarin kare lafiyar yara

Peter Hille ZMA/LMJ
March 7, 2023

Kowane yaro guda daga cikin shida a Jamus yana da nauyi fiye da kima, a kan haka ministan kula da abinci mai gina jiki da aikin gona Cem Özdemir ya ke son haramta tallan duk nau'o'in abinci mai illa ga lafiyar al'umma.

https://p.dw.com/p/4OMun
Jamus | Yara | Abinci mai Gina Jiki
Kokarin kare lafiyar yara a JamusHoto: AP

Ministan kula da abinci mai gina jiki da aikin gona na Jamus din Cem Özdemir dai fuskantar kalubale daga masana'antun sarrafa kayan kwalam da makulashe na kasar, inda suke nuna matukar adawarsu da matakin da yake son dauka din. Idan har Cem Özdemir na jam'iyyar masu rajin kare muhalli ta Green ya cimma nasara, nan ba da jimawa ba za a dakatar da irin wannan tallan. Ministan na son a daina nuna tallan abinci mai illa ga lafiyar al'umma, a lokacin da yara kanana ke gida kuma ido biyu a talabijin da rediyo da kuma Intanet, wanda ke nufin tsakanin karfe shida na safe zuwa 11 na dare. Wannan kuma ya kamata ya shafi mutane masu tasiri a  shafukan YouTube ko Tiktok. Bugu da kari, nan gaba a kwai bukatar a haramta sanya fastocin tallan kayan zaki da abinci mai kitse ko gishiri a cikin launuka masu haske a kusa da makarantu ko wurin renon yara da ma wuraren wasansu.
Özdemir ya kara da cewa tallan kayan abinci mai illa ga lafiyar al'umma, na da tasiri a kan halayyar cin abincin yara. Duk da haka, wakilan masana'antar sarrafa abinci ta Jamus sun musanta hakan. Carsten Bernoth shi ne babban jami'in zartarwa na kungiyar gamayyar masana'antar kayan abinci ta Jamus, kuma a hirarsa da tashar DW ya nunar da cewar haramcin talla ba zai sa yara su rage yawan cin kayan zaki ba. Kamfanonin sarrafa kayan zaki na Jamus sun sanar da cinikin kusan Euro miliyan dubu 14 a bara kadai, kuma sun kashe kusan Euro miliyan dubu daya wajen talla. Bernoth na fargabar cewa matakin na Özdemir za su kai ga kusan dakatar da tallata masana'antarsa, domin hatta tallan da aka yi niyya ga manya wanda yara za su iya gani zai fado karkashin haramcin da aka tsara. Ga misali a kasar Chile, tun a shekara ta 2016 aka kafa dokoki masu tsauri kan tallan alawa ta yara. Tun daga lokacin ne kuma aka fara tattara bayanai kan tasirinsa, inda suka nuna cewa yaran sun juya zuwa wasu nauo'in abinci bayan an haramta tallan.

Cem Özdemir | Minista | Abinci mai gina jiki | Jamus | Aikin Gona
Ministan kula da abinci mai gina jiki da ayyukan gona na Jamus Cem ÖzdemirHoto: Metodi Popow/IMAGO