1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta zuba jari a Iran

Abdul-raheem Hassan
May 18, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da matakan fadada masana'antunsu a kasar Iran, matakin da zai ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran na 2015.

https://p.dw.com/p/2xxKJ
Bulgarien EU-Balkan-Gipfel in Sofia | Jean-Claude Juncker
Hoto: Reuters/S. Nenov

Hukumar kungiyar Tarayyar Turai ta fara wani yunkuri na musamman da zai bullo da sabbin dabarun kafa kamfanoni da masana'antu a Iran, shirin na da zimmar bunkasa tattalin arzikin Iran daga durkushewa bayan da shugaban Amirka Donald Trump ya yi barazanar sake kakaba wa Iran din sabbin takunkumin kasuwanci.

EU ta ce matakin kungiyar zai taimaka wa gwamnatin Tehran damar ci gaba da samun kwarin gwiwar mutunta yarjejeniyar 2015 da aka cimma kan janye sarrafa makaman nukiliya, bayan da Amirka ta juya wa yarjejeniyar nukiliyar baya.

Da yake tsokaci kan matakin bayan kammata taron kungiyar EU a Sofia babban birnin kasar Bulgeriya, Shugaban hukumar Jean-Claude Juncker ya ce "Mun yarda cewa EU za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar, matukar Iran za ta ci gaba itama."