Mata uku sun kai hari a Maiduguri | Labarai | DW | 23.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mata uku sun kai hari a Maiduguri

Mutane 13 sun mutu yayin wani harin kunar bakin wake da wasu 'yan mata uku suka kai a jihar Borno, harin da ya yi sanadiyar jikkata mutane 16.

'Yar kunar baken ta farko ta tarwatsa jigidar bam da ke jikinta ne da misalin 9:15 na daren ranar Lahadi a gaban wani gidan cin abainci. Sauran 'yan kunar bakin waken biyu, sun tashi bama-bamai da ke jikinsu ne jim kadan bayan tashin bam na farko wanda ya jikkata mutane da dama.

Jami'an soji da ke yunkurin fatattakan sauran 'yan kungiyar a Borno, sun ce wadannan jerin hare-hare sun faru ne sa'oi kalilan bayan samun wasu bayanan sirri na silalewar 'yan kungiyar Boko Haram a sassa daban-daban na jihar.

Babu dai wadanda suka dau alhakkin harin kawo yanzu, amma dai kungiyar Boko Haram ta sha ikirarin irin hare-hare makamantan wannan da ke kashe jami'an tsrao da fararen hula sama da 20,000 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.