Jamus: Masu tsattsauran ra'ayi sun karu
July 9, 2020Talla
Ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofer wanda ya gabatar da rahoton a Berlin tare da shugaban ofishin da ke lura da kare kundin tsarin mulki Thomas Haldenwang yace bayanai sun nuna an sami karuwar masu tsattauran ra'ayi a Jamus a shekarar 2019.
A cewar rahoton hukumar sa ido kan bayanan sirri na cikin gida BfV ta gano mutane fiye da 32,000 masu wannan akida ta tsattsauran ra'ayi a shekarar 2019 sabanin mutum 24,100 a shekarar da ta gabace ta.
Tsattsauran ra'ayi da batun wariyar launin fata da kuma akidar kyamar Yahudawa na karuwa a Jamus a cewar ministan cikin gidan Horst Seehofer.
Yace wannan babbar barazana ce ga tsaron kasar Jamus.