1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Martani kan bude kan iyakoki

December 17, 2020

Kasa da 'yan sa'o'i da sake bude iyakokin Tarayyar Najeriya guda hudu, muhawara ta barke cikin tkasar a tsakanin masu tunanin an yi daidai da kuma masu kallon sake bude iyakar ka iya sake haiafar da sabon rikici.

https://p.dw.com/p/3mria
Nigeria Seme Grenze zu Benin
Kan iyakar Seme a Najeriya da ta raba tsakaninta da Jamhuriyar BeninHoto: Reuters/A. Sotunde

Kama daga tattali na arziki zuwa ga zamantakewar al'umma dai, wattanin 16 na iyaka a rufe sun yi tasiri a tsakanin al'umma dabam-dabam cikin Tarayyar Najeriyar. Kuma cikin tsawon kasa da sa'o'i 24 da sake bude iyakokin guda hudu, Najeriyar ta dauki dumi bisa matakin 'yan mulkin na sake gwajin bude kasar.

Karin Bayani: Martanin makwabta kan ci gaba da rufe iyakokin Najeriya

Duk da cewar dai ba su ambato hujjojin dauka na matakin ba, daga dukkan alamu wani kwamiti na gwamnati a karkashin ma'aikatar kudin kasar ya kai ga shawarar da shugaban kasar ya amince kanta. Kasa da makonni biyun da ke tafe ne dai za a kaddamar da kasuwanci mara shinge a daukaci na kasashe na nahiyar Afirka, abun kuma da ke nufin bude iyakar ga kasar da ta rattaba hannu cikin yarjejeniyar da za ta samar da kasuwa mafi girma a duniya baki daya.

Karin Bayani: Cece-cuke kan rufe iyakokin Najeriya

Abujar dai ta karya kumallo da bude wasu iyakoki guda hudu, kafin ya zuwa karshen watan da muke ciki ta bude daukacin iyakokin kasar, domin ciniki. Matakin kuma da ya bata ran wasu a ciki na masu kasuwar da ke amfana da tsarin iyaka a rufen da kasar ta share wattani 16 tana fuskanta. Mr Peter Dama na zaman shugaban kungiyar kananan masu sarrafa shinkafa  ta kasar da kuma ya ce akwai bukatar taka tsan-tsan da nufin kauce jefa masu kasuwar kasar cikin halin rikici.

Nigeria Grenze zum Niger
Kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar NijarHoto: DW/Y. Ibrahim

To sai dai in har bude iyaka na iya kai wa ga jefa masu shinkafar Najeriyar cikin matsala mai girma, ga ragowar 'yan kasuwar kasar dai bude iyakar na kama da Babbar Sallah, a fadar Saratu Aliyu da ke zaman shugabar kungiyar kananan 'yan kasuwar Najeriyar NACCIMA. Ko bayan ciyar da kan da ke zaman babban kwazo dai, babban burin rufe iyakokin  na zaman kai karshen fasa kwauri dama shigar kanana na makamai cikin kasar.

Karin Bayani: Martanin kan hana shigo da motoci ta kan iyakar Najeriya

Sai dai kuma an kai har ga bude iyakar daga dukkan alamu kuma a fadar Abubakar Ali da ke zaman masanin tattalin arzikin  kasar ba tare da cika buri na kulle iyakokin ba. Dole kanwar naki ko kuma kai wa ga bukata dai, in har masana na da tunanin an bata lokaci da matsawa al'umma, Abujar na kallon matakin da ta dauka na rufe iyakokinta da idanun nasara a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin gwamnatin tarayyar. Akalla dalar Amirka miliyan dubu biyar ne dai gwamnatin kasar ta ce ta tserar, daga kai karshen tsohuwar al'adar shigo da hajjar shinkafa cikin kasar.