1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharudan Najeriya dangane da bude iyakokinta

February 23, 2020

Hukumomi a Najeriya sun bukaci rushe daukacin rumbunan ajiye kaya da ke a kan iyakar Najeriya da kasashen Benin da na Niger kafin kaiwa ga bude iyakokin da ke tsakanin kasashen.

https://p.dw.com/p/3Y9jV
Nigeria Seme Grenze zu Benin
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Gwamnatin ta Najeriya ta ambata hakan ne 'yan sa'o'i kalilan bayan ganawa da shugaban kasar Burkina Fasa Roch Marc Kabore da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a Fadar Aso Rock. Kabore dai ya zanta da Buharin ne a wani kokari na lallashinsa don ya bada damar shigo da kayayyakin da suke iya lalacewa daga kasashe makwabtan a matsayin matakin farko na kaiwa ga kawo karshen rufe iyakar kasar mai tasiri a yammacin Afirka.

Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen
Kasashen ECOWAS na son ganin Najeriya ta bude kan iyakokintaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

To sai dai kuma Tarrayar Najeriyar ta ce ya zama wajibi a rushe daukacin rumbunan ajiyar kaya da ke a kusa da iyakar kasar da kasashen Benin da Nijar sannan kuma da karba ta rahoton wata runduna ta hadin gwiwa da ke sintiri a kan iyakar kasashen uku kafin yanke hukuncin karshe game da batun.

Har wa yau, shugaban na Najeriya ya nunawa bakon nasa cewar akwai dalilai da kalubale da suka kai ga rufe iyakar wadanda suka hada da shigo da shinkafa da kananan makamai da kuma muggan kwayoyi da ke barazana ga kasar. Haka ne ma ya sanya Najeriyar inji shugaban auna tsakanin batun tsaronta da kuma yarjejeniyar ciniki ta yankin na yammacin Afirka.