1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An yi karin haske kan shigo da shinkafa

October 4, 2016

Hukumar hana fasakwauri a Najeriya ta bayyana cewa dalilan da suka sanya takaita shigo da shinkafa kasar a daidai lokacin da ake ci gaba da kace na ce a kan wannan batu da ya sanya fuskantar tsadar shinkafa a kasar.

https://p.dw.com/p/2Qs5J
Reisanbau in Nigeria
Hoto: DW/S. Duckstein

Kace-nace da ake cigaba da yi a kan wannan batu da ya biyo bayan tsadar da shinkafar ke yi a Najeriyar ya sanya hukumar ta Kwastam fitowa fili ta bayyana matsayinta domin fayyace matakan da ta dauka, inda ta ke cewar ta yi wanan yunkuri ne don kare  lafiyar al'ummar Najeriya da ma kananan manoman kasar. Kanar Hameed Ibrahim Ali mai ritaya da ke zaman shugaban hukumar ya ce ''gwamnati ba ta hana shiga da shinkafa Najeriya ba, wanda aka hana shi ne wadda akae shigarwa ta kan tudu saboda a kan samu wanda ke shigar da gurbatacciya ta wadannan hanyoyi.''

An dai nunawa ‘yan jaridu majigi na hanyoyi mabambanta da masu fasa kwauri ke bi suna shiga da shinkafa kasar wadanda suka hada da cusa ta a karakshin batirin mota da sauran wurare marasa tsafta don batar da sawu da nufin bi da su ta kan iyakokin kasar da ke kan tudu. Da ta ke tsokaci kan wannan batu, Yetunde Oni wadda ke jagorantar hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta Najeriya ta ce ''alkaluma sun nuna cewa shinkafar da aka yi fasakwaurinta ta kan iyakokin Najeriya na tudu ba su da inganci kuma ba a yi masu rijista ba domin an boye su a wuraren da ba su dace ba''.

Najeriyar dai na shigo da tan miliyan 3 ne na shinkafa kuma bayanan na nuna cewa a bana za ta samar da kusan tan miliyan biyu a cikin kasar, abinda ya sanya dakile duka hanyoyin fasa kwauri da ke illa ga tattalin arzikin kasar da ke fuskantar koma baya. Malam Dahiru Ado Kurawa da ke kula da kwamitin lura da fasakwauri a Najeriyar ya ce ''mtakanin hana shiga da shinkafa Najeriya ta kan tudu lamari ne da zai taimaka wajen samawa 'yan kasa aiki da ma bunkasa tattalin arzikin kasar wanda ya shiga yanayi na masassara.''