Mali ta ce ta samu nasarar kawar da Ebola | Labarai | DW | 19.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali ta ce ta samu nasarar kawar da Ebola

Mahukuntan Mali sun ce kasarsu ta shiga jerin kasashen da suka samu nasarar kawar da cutar nan ta Ebola da ta yi ta'adin gaske a wasu kasashen yammacin Afirka.

Ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Ousmane Kone ne ya bayyana a jiya Lahadi inda ya ke cewar kasar ta shafe kwanaki 42 ba tare da samun labarin wanda ya kamu da cutar ba, matakin da ke nuna cewar babu cutar a kasar baki daya.

A cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai kasar ta Mali ta ce an samu mutum na farko da ya kamu da cutar, inda jimillar mutane 8 suka kamu, shidda daga cikinsu suka gamu da ajalinsu kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta WHO ta shaida.