Malala Yousafzai ta isa a kasarta ta Pakistan | Labarai | DW | 29.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Malala Yousafzai ta isa a kasarta ta Pakistan

Malala Yousafzai, ta isa a birnin Islamabad na kasar Pakistan a karon farko tun bayan da 'yan kungiyar Taliban suka kai ma ta hari a shekara ta 2012.

Malala Yousafzai

Malala Yousafzai ta sauka a birnin Islamabad na Pakistan

Wannan dai shi ne karo na farko da Malala ta isa a wannan kasa tata ta haihuwa, tun bayan da 'yan kungiyar Taliban suka harbeta da bindiga bisa kai a shekara ta 2012. Inda aka fice da ita ya zuwa birnin London na Birtaniya aka yi ma ta magani, sannan ta ci gaba da karatunta. Da yake magana kan wannan ziyara ta Malala a kasar ta Pakistan, mai magana da yawun ofishin ministan harkokin wajen kasar Muhammad Faisal, ya ce suna masu yin maraba da zuwan Malala a gida Pakistan, inda ya kara da cewaR matashiyar mai shekaru 20 da haihuwa da ke fafutikar kare incin ilimin diya mata, za ta gana da mutane da dama a kasar, sai da kuma ba a sanar da wuraran da za ta bi ba ta sabili da dalillai na tsaro.