Kyautar Nobel kyauta ce da ake baiwa wadanda suka yi fice a fannin samar da zaman lafiya da kuma kare hakkin dan Adam.
A cikin shekarar 1901 ne aka fara bada kyautar Nobel. Wani dan kasar Sweden mai suna Alfred Nobel ne ya umarci a yi amfani da dukiyarsa bayan rasuwarsa don girka wata gidauniya da za ta rika baiwa mutunen da suka yi fice kyautar ta Nobel a kowacce shekara.