1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pääbo ya samu Nobel ta fannin likitanci

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 3, 2022

An bayar da kyautar Nobel ta fannin likitanci ga wani gwarzon masanin kiwon lafiya dan asalin kasar Sweden Svante Pääbo bisa binciken da ya yi kan halitun dan Adam.

https://p.dw.com/p/4HgqA
Forscher Svante Pääbo
Hoto: Christian Charisius/dpa/picture alliance

Wannan likita Svante Pääbo mai shekara 67 a duniya da ke da zama a tarayyar Jamus, ya kaddamar da gwaje-gwajen kwayoyin hallitar bil'Adama shekaru 13 da suka gabata masu nasaba da tushen mutum fiye da shekaru dubu 30, kana ya gano cewa asalin gangar jikin dan Adam yana kunshe da sanadarin da ke ba wa garkuwar jiki kwarin gwiwar jajircewa wasu cututuka.

Svante Pääbo dai, shi ne kwararren likita na 113 da ya samu kyautar Nobel a tarihi, a daura da wasu masana 226 da suka kunshi masu bincike kan fannoni da suka jibanci bani Adama ciki har da mata 12.