1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Kamaru na yakar Boko Haram

February 4, 2015

Dakarun kasar Kamaru sun hallaka akalla mayakan kungiyar Boko Haram 50 a wata bata kashi da suka yi da su a garin Fotokol na Kamarun da ke kan iyaka da Najeriya.

https://p.dw.com/p/1EVjS
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Minstan yada labaran kasar ta Kamaru Issa Tchiroma ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters hakan, inda ya ce sojojojin Kamarun shida suma sun rasa rayukansu a yayin fafatawar da suka yi da 'yan Boko Haram din da ke gwagwarmaya da makamai a makwabciyarsu Tarayyar Najeriya. 'Yan Boko Haram din dai sun kadddamar da hari ne a kan garin na Fotokol wanda ya haddasa mummunan bata kashi a tsakaninsu da sojojin na Kamaru. Rahotanni sun nunar da cewa a jihar Arewa Mai Nisa ta Kamarun ma 'yan Boko Haram din sun karkashe mutane ta dama yayin da suka shiga gidaje da kuma masallaci suka yanka wasu, sai dai da aka tuntube shi Tchiroma ya ki cewa komai a kan wannan batu inda ya ce suna jiran rahoto daga ma'aikatar tsaron kasar tukunna.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu