Majalisar Girka ta amince da matakin tsuke bakin aljihu | Labarai | DW | 16.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Girka ta amince da matakin tsuke bakin aljihu

Sabbin matakan tsuke bakin aljihun sun tanadi kara kudin haraji da takaice kudin pansho da sake tsarin yadda kasar ke yin kasafin kudinta.

Majalissar dokokin kasar ta Girka ta amince da bukatar da Firaminista Alexis Tsipras ya gabatar mata duk da zanga zangar da wasu 'yan kasar su kimanin dubu 12 suka gudanar domin nuna adawarsu da shirin gwamnatin.

Amincewa da sabbin matakan da kasar ta Girka ta yi, na a matsayin wani tsanin farko na cika sharuddan da Kungiyar Tarayyar Turai da asusun bada lamani na duniya na IMF suka gindaya mata kafin sake bata wani bashin na kudi kimanin miliyon dubu 80 na euro a na gaba.