Mahmud Abbas ya ziyarci Berlin | Siyasa | DW | 18.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahmud Abbas ya ziyarci Berlin

Shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta karbi bakuncin shugaban Palesdinawa Mahmud Abbas a Berlin, domin tattauna batun zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya

A lokacin wata ziyara da shugaban Palesdinawa Mahmud Abbas ya kai birnin Berlin, shugaban gwamnati Angela Merkel ta tabbatar masa da cewar Jamus zata ci gaba da bin manufofin da tuni ta shimfida game da yankin gabas ta tsakiya. Merkel ta kuma nunar da cewar gwamnatinta zata ci gaba da baiwa Palesdinawan taimako a fannin tattalin arziki, tare da kokarin ganin an aiwatar da manufar nan ta samarwa Palesdinawa yantacciyar kasar kansu da zata zauna kafada da kafada da Israila.

Fafitikar da ake yi ta neman kafa sabuwar gwamnatin taraiya ta hadin gwiwar jam'iyu bayan zabe, shine babban abin da yafi daukar hankali yanzu a Berlin. Saboda haka yan jarida kalilan ne suka hallara da safiyar Jumma'a a wurin taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin shugaban gwamnati, Angela Merkel da shugaban Palesdinawa Mahmud Abbas. Bai kuwa zama abin mamaki ba ganin cewar tambayar farko ta shafi kokarin ne na kafa gwamnatin hadin giwa a babban birnin na Jamus a shawarwarin da za'a fara mako mai zuwa tsakanin jam'iyun CDU da CSU da kuma SPD, tare da nemn sanin ko manufofin ketare na gwamnatin tarayya zasu canza, idan har aka kafa gwamnatin hadin gwiwa ta manyan jam'iyun. To sai dai shugaban gwamnati Angela Merkel tace babu abin da zai canza a manufofin ketare da gwamnatinta tuni ta shimfida. Tace gwamnatin da wa'adin ta zai cika a mako mai zuwa tuni ta baiyana goyon baya ga kokarin samarwa Palesdinawa yantacciyar kasarsu ta kansu da zata zauna kafada da kafada da kasar Israila ta hanyar shawarwarin lumana. Tace gwamnatinta zata kuma ci gaba da goyon baya da taimakawa Palesdinawan a fannin tattalin arziki da kudi.

A shawarwarin ta da Mahmud Abbas, Merkel ta nunar masa a fili cewar shawarwarin lumana ne kadai zasu iya taimakawa a kai ga sulhunta rikicin yankin na gabas ta tsakiaya. Shugaban gwamnatin tayi kira ga Israila ta dakatar da manufofinta na ci gaba da gina matsugunan Yahudawa a yankunan Palesdinawa da ta mamaye.

Tace Muna kuma kira ga Israila ta janye manufofinta na gina matsugunan Yahudawa a yankunan Palesdinawa da ta mamaye.

Israel Palästina Grenze

Iyaka tsakanin Israila da Palesdinu

A wannan shekara ta 2013, gwamnatin taraiya ta Jamus ta taimakawa yankunan Palesdinawa da kudi misalin Euro miliyan 100, kuma nan gaba ma wannan taimako ba zai yanke ba, inji Merkel, saboda yana da muhimmanci mazauna yankunan na Palesdinawa su kasance masu cin gajiyar bunkasar tattalin arziki a yankunan. To sai dai ana bukatar zuba jari a can, yadda tsarin tattalin arzikin zai farfado har ya sami bunkasar da ake so.

Mahmud Abbas yayi godiya ga irin taimakon tatalin arziki da Jamus ta baiwa Palesdinawan da kuma taimakon da zata ci gaba da bayarwa nan da shekaru masu zuwa. Yace wajibi ne kuma a binciko hanyoyin jan hankalin yan kasuwa su kara yawan jaridun da suke zubawa a yankunan na Palesdinawa, saboda Palesdinawan suna bakin kokarinsu game da neman sulhu tare da Israila. Tilas ne mu yi amfani da dama ta tarihi da ta samu domin kaiwa ga sulhu, inji shi. Batun neman zaman lafiya tsakanin Israila da Palesdinawa ya tsaya gaba daya a yan shekatrun nan, to amma a watan Agusta bangarorin biyu suka sake komawa kan teburin shawarwari karkashin jagorancin sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry. Shugaban na Palesdinawa yayi korafin cewar Israila ta kara tsananta giggina matsugunan Yahudawa a yankunan da ta mamaye.

Symbolbild Israel Palästina Siedlungsbau

Katangar da ta raba matsugunan Yahudawa da yankunan Palesdinu

Yace a kullum muna goyon bayan samun kasashenmu biyu da zasu zauna kafada da kafada da juna, a kullum muna kokarinmu na ganin mun bunkasa yankunan Palesdinawa, mu kuma baiwa wadannan yankuna goyon baya, muna taimakawa kokarin samar da zaman lafiya. Zamu ci gaba da bin wadannan manufofi zamu kuma fadada su.

A bisa kiyasin wata kungiyar zaman lafiya ta Israila mai suna Peace Now, gina matsugunan na Yahudawa ya karu da kashi 70 cikin dari a shekara ta 2013. Kungiyar tace Israila tilas ta dakatar da wadannan gin-gin, wadanda bisa kudirin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, gine-gine ne na haramun.

Mawallafi: Naomi Conrad/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin