Mahakar zinare ya rufta da mutane a Maradi | Labarai | DW | 01.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahakar zinare ya rufta da mutane a Maradi

Rahotanni daga jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar na cewa akalla mutane shida sun sake mutuwa bayan ruftawar kasa a wata mahakar zinare a garin Kwandago da ke karamar hukumar Dan Issa a ranar Litinin.

Bayanai daga yankin na nuna cewar Mahakan na bi ta barauniyar hanya suna bada cin hanci ga jami'an tsaron da ke kula da mahakar tun bayan mutuwar mutane da dama a shekarar 2021. "Me ya kai farar hula wurin da ake tsaro, har su shiga rami kasa ya rufta da su in babu hadin baki da sojojin da ke aiki a wurin" a cewar Gwamnan jahar Maradi Malam Shaibu Abubakar.

A shekarar 2021, an tabbatar da mutuwar mutane akalla 18 bayan da rami ya rufta da masu hako zinare a wannan yankin, matakin da ya sa hukumomi killace wurin saboda kare lafiyar al'umma.