Mafi yawan Rashawa dai na ganin cewa, zaben shugaba kasar da za a yi a cikin watan ... | Siyasa | DW | 12.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mafi yawan Rashawa dai na ganin cewa, zaben shugaba kasar da za a yi a cikin watan ...

Maris mai zuwa, ba shi da wata ma'ana. Dalilin haka kuwa, shi ne, shugaba Putin ya mamaye komai. Tun kafin ma a shirya tsarin zaben, kowa ya san cewa, shugaban da mukarrabansa ne za su zarce da mulki. Wani marubucin Rashan, Viktor Jerofejew, ya rubuta wata almara inda ya kikiro wani mutum mai adalci, wanda kuma yake cika duk alkawarin da ya dauka. To wannan mutumin kadai ne zai iya tsayawa takara da shugaba Putin, ya kuma lashe zaben. Amma a kashin gaskiya, babu shi sai dai a cikin almaran da Jerofejew ke rubutawa a cikin jaridun Moscow.

A halin yanzu dai, a zayyane, `yan takara guda 9 ne za su kalubalanci shugaban na Rasha. Amma dukkansu, ba su da wani muhimmanci a fagen siyasan Rashan. Akwai dai mutane kamarsu Sergei Mironow, wanda ake ganin ya shiga takarar ne kawai don a nuna wa duniya cewa, da akwai masu niyyar kalubalantar shugaban da gaske. Shi dai Mironow, dan hannun daman shugaba Putin ne. Sabili da haka ne kuwa masu sukar lamiri ke bayyana ra'ayin cewa, shiri kawai aka yi na tura shi tsayawa zaben.

A zaben mjalisar kasar da aka yi a cikin watan Disamba ma, sai da kugiyar tsaro da ma'ammala a nahiyar Turai, wato OECD ta yi kakkausar suka ga yadda aka gudanad da shi. Ba a dai nuna adalci a zaben ba inji kungiyar. A lokacin kirga kuri'un da aka ka da kuma, an yi ta tabka magudi. Sabili da haka ne kuwa, sahihan `yan takara da da can suka yi niyyar tsayawa a zaben shugaban kasar suka janye. Duk muhimman kafofin yada labaran kasar dai, karkashin ikon fadar Kremlin suke. Ta hakan ne kuwa, ake ta ci wa duk wanda zai iya kasancewa barazana ga shugaba Putin mutunci a talabijin da Rediyo. Idan hakan mka bai wadatas ba, to sai a kirkiro wani laifi, wanda za a ce dan takarar ya akata, kamar dai yadda aka dora wa shugaban kamfanin hakon man nan na Rasha, Michail Chodorkowski, laifin keta dokokin harajin kasar. Tun wannan lokacin ne dai yake tsare a kurkuku. Kuma bisa dukkan alamu, ba za a sako shi ba sai bayan zaben.

Wannan halin da ake ciki ne kuwa, ya sa `yan takara da dama suka ki ma rajistan sunansu don tsayawa a zaben. Grigorij Jawlinski, shugaban jam'iyyar nan ta Jabloko na cikin wadanda suka dau wannan matakin.

Ana nan dai ana jira a gani ko daga baya, wani zai fito ya nuna sha'awarsa na tsayawa a zaben ban da shugaba Putin. Tun da dai kowa ya san, an shirya cewa shugaban ne zai lashe zaben, to mai yiwuwa, jama'a da yawa ma su kaurace wa zuwa ka da kuri'unsu. Bisa ka'ida dai, idan kasa da kashi 50 cikin dari na masu ka da kuri'an ne kawai suka halarci zaben, to sai a soke shi gaba daya, a sake wani zaben kuma. Amma wata ka'idar kuma ta ce duk wanda ya tsaya a karo na farko, inda aka sami karancin masu ka da kuri'u, ba shi da damar sake tsayawa. To ke nan, idan aka sami yawan masu jefa kuri'u kasa da kashi 50 cikin dari, shugaba Putin ba shi da damar sake tsayawa ke nan. Sabili da haka, ko ta yaya mahukuntan fada Kremlin za su yi duk iyakacin kokarinsu wajen ganin cewa, an sami masu jefa kuri'u fiye da kashi 50 cikin dari, ko da ma da magudi ne. Idan ko hakan ya auku, to kwarjinin shugaban a ketare zai dusashe.

Yanzu dai, saura wata biyu a yi zaben na Rasha. Masu bai wa shugaba Putin shawara ne kawai suka san yadda ababa za su kasance. Kafin wannan lokacin kuwa, duk duniya na sa ido ne ta ga yadda ababa za su wakana.