Macron da Poroshenko sun yi fatan kawo karshen rikicin Ukraine | Labarai | DW | 26.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron da Poroshenko sun yi fatan kawo karshen rikicin Ukraine

Shugabannin biyu na sa ran shirya wani taro kan Ukraine ko dai a karshen wannan wata na Yuni ko kuma a farkon watan Yuli.

Frankreich Emmanuel Macron & Petro Poroschenko (Reuters/P. Wojazer)

Petro Poroshenko da Emmanuel Macron a birnin Paris

A wannan Litinin shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sake jaddada kudurinsa na goyon bayan yarjeniyoyin birnin Minsk da ke da burin gano bakin zaren warware rikicin kasar Ukraine.

Macron ya nuna hakan ne a wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi a birnin Paris da takwaran aikinsa na Ukraine Petro Poroshenko. Macron ya kuma kara da cewa Faransa ba za ta amince da matakin da Rasha ta dauka na shigar da yankin Kirimiya a cikin kasar ba.

Ya ce: "Kamar yadda na sha nanatawa a hirarrakinmu ta wayar tarfo da ma a bainar jama'a, na sake ba wa Shugaba Poroshenko tabbacin cewa zan ci gaba matsa kaimi don ganin an yi aiki da yarjejeniyar Minsk. Ina kuma fata za a yi hakan gababin taron kungiyar G20. Ita ma shugabar gwamnatin Jamus abinda take so ke nan, wato tattaunawar da za ta kai mu gaci."

Macron da Poroshenko sun ce suna sa ran shirya wani taro kan Ukraine tsakanin Jamus da Faransa da Ukraine da kuma Rasha ko dai a karshen wannan wata na Yuni ko kuma a farkon watan Yuli.