1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lig-lig na Turai da jifan tama a Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 3, 2018

A shirin na wannan lokaci za mu leka wasannin Lig-lig na Turai. Koriya ta Kudu ta lashe kofin kwallon kafa na wasannin tsalle-tsalle na Asiya da aka yi a birnin Jakarta.

https://p.dw.com/p/34DZD
Fußball Bundesliga RB Leipzig - Fortuna Düsseldorf
Hoto: Getty Images/AFP/R. Michael

Bari mu bude shirin da wasannin kwallon kafar kasar Jamus na Bundesliga inda a karshen mako aka buga wasannin mako na biyu, inda a yayin da kungiyoyi kamar su yaya babba cewa da Bayern Munich da Wolfsburg da Hertha Berlin suka yi nasarar lashe wasanninsu biyu da suka buga wasu daga cikin kungiyoyin wadanda ga al'ada suka saba shiga gasar da kafar dama irin su Shalke04 da matashin mai horas da 'yan wasanta Dominico Todesco da kuma Leverkusen na ci gaba da yin sakarsu da mugun zare inda ko a wannan mako suka sha kashi a gidansu daya bayan daya. A yanzu dai kungiyar Bayern Munich ce ke a saman teburin na Bundesliga da maki shida, Wolfsburg wacce da kyar da jibin goshi ne ta kwaci kanta a kakar wasannin a bara, a yanzu tana matsayin ta biyu da maki shida kana Hertha Berlin na matsayin ta uku da maki shida ita ma.

Mateo Kovacic
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Grant

A Ingila ma a karshen mako an buga wasannin mako na hudu na gasar Premier Lig, inda nan ma kungiyoyi uku wato Liverpool da Chelsea da Warford ne a halin yanzu ke  gosilo a saman tebirin bayan da suka yi nasarar lashe wasanni hudu. Kungiyar Liverpool ta bi Leicester har gida ta kuma doke ta da ci biyu da daya. Dan wasan kasar Senegal Sadio Mane shi ne ya zura kwallon farko mintuna 10 da soma wasa. Daga nata bangare kungiyar Chelsea ta karbi bakuncin kungiyar Bournemouth ne ta kuma doke ta da ci biyu da babu, yayin da kungiyar Watford ta karbi bakuncin Tottenham ta kuma lashe ta da ci biyu da daya. Kungiyar Man United wacce ta soma sakar tata ta bana da mugun zare, ta fidda wa kanta kitse a wuta a wannan mako bayan da ta bi Burnley har gida ta kuma doke ta da ci biyu da babu. A yanzu dai kungiyar Liverpool ce ke kan teburin na Premier Lig da maki 12 sai Chelsea a matsayin ta biyu da maki 12 ita ma, haka ma Watford na da maki 12 a matsayin ta uku a kan teburin.

Yanzu kuma sai kasar Spain inda a wannan mako aka fuskanci ambaliyar ruwan kwallaye a wasannin mako na uku na gasar La Liga. Bayan da a ranar Asabar kungiyar Real Madrid ta yi zazzaga ga Legane da ci hudu da daya a Bernabeu, a ranar Lahadi Barcelona ta kidima sabon shiga Kungiyar Huesca da ci takwas da biyu. Kungiyar ta Huesca ce dai ta fara tsokano tsuliyar dodo inda kusan ba zato ba tsammani ta fara da zura wa Barecelona kwallo mintoci uku kacal da fara wasa a gaban dubban 'yan kallo a filin wasan na Noucamp. Wannan kwallo da suka zura ta kasance tamkar sun tabo gidan rina inda kafin a kammala wasan suka gane kuransu, inda suka kwashi har kwallaye takwas. A yanzu dai Kungiyar ta barecelona ce ke saman teburin na La Liga da maki tara, kishiyarta ta Madrid na bi mata ita ma da maki tara a yayin da ke Celta ke a matsayin ta uku da maki bakwai.

La Liga Deportivo La Coruna v Barcelona Messi
Hoto: Getty Images/D. Ramos

Yanzu kuma sai wasannin tsalle-tsalle na nahiyar Asiya karo na 18 wadanda aka kammala a ranar Lahadi a kasar Indonesiya. Biranen Jakarta da Palembang ne suka karbi bakuncin wasannin na bana, inda 'yan wasa daga kasashe 45 na Asiya suka fafata a nau'o'in wasannin 34 da suka hada da kwallon kafa da damben zamani da ninkaya da kwallon zari ruga da kwallon hannu da kwallon raga da dai sauransu. A fannin kwallon kafa dai Koriya ta Kudu ce ta lashe kofin wasannin bayan da ta doke Japan da ci biyu da daya. Sai dai a Jumulce Chaina ce ke sahun gaba da tammaye 16 da suka hada da bakwai na zinariya. Japan na bi mata da tammaye 14 uku na zinare. Koriya ta Kudu na a matsayin ta uku da tammmaye 10 biyu na zinare.

A Jamhuriyar Nijar kuwa a karshen mako a birnin Tahoua aka gudanar da gasar cin kofin kasa na wasannin jifar tama ko kuma petaque da Turancin Faransa. A sauran wasanni kuma a ranar Lahadi aka kammala wasan tseren motoci na Formula One na Grand Prix d'Italie. Kuma dan kasar Birtaniya da ke tuka wa kamfanin Mercedes mota wato Lewis Hamilton ne ya lashe gasar a cikin sa'a daya da mintuna 16 da dakika 54. A ranar Lahadin ne kuma dan kasar Rasha Sergey Shubenkov ya lashe gasar gudun tsallen shinge na mita 100 a birnin Padoue na kasar Italiya a cikin mintuna 13 da dakika tara.