libiya: Sama da bakin haure 100 sun kife a ruwa | Labarai | DW | 25.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

libiya: Sama da bakin haure 100 sun kife a ruwa

Hukumomin Libiya sun tabbatar da bacewa akalla bakin haure 115 bayan da kwale-kwale dauke da mutane 250 ya kife a gabashin birnin Tripoli.

Jami'an da ke tsaron gabar ruwa a Libiya sun tabbatar da mutuwar mutum daya yayin da aka ceto mutane 134 da suka fada ruwa, yawancin wadan da aka ceto 'yan kasashen Afirka ne da Larabawa. Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM ta kiyasata bakin haure 426 sun mutu a tsakiyar tekun bahrum a shekarar 2019 ka dai a yunkurin shiga nahiyar Turai.