Lavrov da Kerry sun tattauna kan rikicin Siriya | Labarai | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lavrov da Kerry sun tattauna kan rikicin Siriya

Rasha dai na shan suka dagane da farmakin da take kai wa IS a Siriya, amma yanzu ana kokarin hana aukuwar wani akasi da Amirka da ita ma ke kai farmaki a Siriyar.

USA UN PK Lawrow / Kerry Treffen Nahost-Quartett in New York

Lavrov da Kerry a taron kasashen neman sulhun Gabas ta Tsakiya a New York

Ministan harkokin wajen Rahsa Sergei Lavrov da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a kasar Siriya. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayar ta ce mutanen biyu sun yi musayar yawu kan yadda za a tuntubi juna a yakin da ake yi da kungiyar IS don hana aukuwar wani akasi musamman a sararin samaniyar kasar ta Siriya, inda jiragen yakin Rasha da Amirka ke shawagi a bama-baman da suka jefawa kan sansanonin kungiyar ta IS.