1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manchester ta doke Tottenham a wasan premier lig na Ingila

Suleiman Babayo AMA
March 14, 2022

Manchester United ta lallasa Tottenham 3 da 2 wasannin lig na kasar Ingila a yayin da Bayern Munich ta yi kunnen doki da Hoffenheim a gasar Bundesliga.

https://p.dw.com/p/48SB1
Fußball | Premier League | Manchester United - Tottenham Hotspur | Cristiano Ronaldo
Hoto: Naomi Baker/Getty Images

A wasannin premier lig na Ingila kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta lallasa Tottenham 3 da 2, kuma dan wasa Cristiano Ronaldo ne ya jefa duk kwalloye ukun a raga, Arsenal ta doke Leicester ci biyu da neman, kana Chelsea ta samu nasara kan Newcastle ci daya mai ban haushi, Leeds ta doke Norwich 2 da 1. 

A wasannin lig na Bundesliga a Jamus, kungiyar Union Berlin ta tashi 1 da 1 da kungiyar Stuttgart,  Dortmund ta doke Arminia 1 da nema, a yayin da Moechengladbach ta samu galaba kan Hertha Berlin 2 da nema, yayin da Hoffenheim da Bayern Munich suka tashi 1 da 1, a teburin Bundesliga, kungiyar Bayern Munich ke jagoranci da maki 60, yayin da Dormund ke matsayi na biyu da maki 53, a matsayi na uku akwai kungiyar Leverkussen da maki 45.

Fußball Bundesliga | Eintracht Frankfurt - VfL Bochum
Hoto: Christian Kaspar-Bartke/Getty Images

A wasanin La Liga na Spain da ake kira La Liga, kungiyar Barcelona ta yi raga-raga da Osasuna 4 da nema, inda Levante da Espanyol suka tashi 1 da 1, kana Villarreal ta doke Celta 1 da 0.

A yankin kudu maso yammacin Najeriya matasa kamar sauran na kasashe masu tasowa na ci gaba da amfani da kwallon kafa a matsayin hanyar fita daga kangin da suka samu kansu kuma hanyar ci-gaba mai dorewa, a jihar Lagos da ke kan gaba wajen habakar kasuwanci, matasa kan fito suna wasannin kwallon kafa a duk inda ke da kananan filayen wasannin kwallo a wani yunkuri na ganin wasan ya zame masu abin dogaro.

A wasannin kwallon Cricket na mata na duniya a Naw Zealand, kasar Bangladesh doke Pakistan yayin karawa tsakanin kasashen biyu.