1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Labarin wasannin daga sassan duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 7, 2020

Bayern Munich na ci gaba da kasancewa a saman teburin Bundesliga a yayin da Youssoufa Moukoko na Dortmund ya zama abin alfahari a Kamaru da yadda ta kaya a fafatawar da aka yi a gasar Confederation Cup na Afirka.

https://p.dw.com/p/3mKHV
Deutschland Frankfurt | Bundesliga | Eintracht Frankfurt v Borussia Dortmund
Hoto: Alex Grimm/Getty Images

Zagaye na biyu na wasannin share fagen shiga matakin rukuni-rukuni na gasar neman lashe kofin zakarun Afirka da aka fi sani da Champions League ya gudana a ranakun Jumma'a da Asabar da Lahadi da suka gabata a kasashe dabam-dabam na wannan nahiya. Wasanni akalla hudu ne ba su gudana ba bisa dalilai dabam-dabam, lamarin da ya haifar da shakku kan makomar gasar ta zakaru. Kungiyar Stade Malien ta haye ba tare da yin wasa ba, saboda abokiyar hamayyarta Ashanty GB ta Guinea ta gaza samun 'yan wasa 16 kamar yadda ka'idodin CAF suka tanada sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 da hudu daga cikin 'yan wasanta suka yi.

Hakazali wasa tsakanin Mouloudia Alger ta Aljeryia da Buffles ta Jamhuriyar Benin bai gudana ba saboda rashin hallaran wakilan na Benin. A wannan Litinin ne hukumar kula da gasar zakarun Afirka wato CAF za ta yanke hukunci kan wannan wasa, inda take da zabi tsakanin dage wasan ko kuma ta yi bayyana Mouloudia a matsayin wacce ta ci bulus. Yayin da a nata bangaren Mekelle 70 Enderta ta Habasha ta ya da kwallo sakamkakon rikicin siyasa da kasarta ke fama da shi, lamarin da ya ba wa Ahli ta Benghazin Libiya damar hayewa. ITa ma Gazelle ta Chadi ta kai bantenta ba tare da wani kare bin damo ba saboda Siaf ta Djibouti ta ce ba ta da damar hallara ba.

CAF Champions League - Finale
Gasar Confederation Cup a AfirkaHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

A sauran wasannin kuwa, El Merreikh ta Sudan ta sake yin nasara kuma ta tsallake zuwa matakin rukuni bayan da ta doke AS Otoho ta Kwango da ci 2-0. Ita ma daya kungiyar da ke wakiltar Sudan Al Hilal ta kai labari bayan da ta doke Vipers ta Yuganda da 1-0. Ita da As Sonidep ta Nijar ta yi abin kai, inda ta lallasa Mogadishu City ta Somaliya da ci 2-0. Sai dai kuma Plateau United ta Najeriya da Simba Sc ta Tanzaniya sun tashi wasa ba tare da wani ya ci kwallo ba, lamarin da ya sa aka yi waje road da wakiliyar ta Najeriya bisa la'akari da sakamakon wasan zagayen farko. Sauran kungiyoyin da suka yi nasarar hayewa matakin rukuni- rukuni na kofin zakarun Afirka sun hada da Gor Mahia ta Kenya da Nkana ta Zambiya, sai Platinium ta Zimbabwe da Club Sfaxien ta Tunisiya da AS Bouenguidi Sports ta Gabon, sai Atletico ta Luandan Angola, da Akso ta Togo sai Belouizdad ta Aljeriya da Teunguetg ta Senegal da kuma Kaiser Chiefs ta Afirka ta Kudu da ta doke PWD da ke rike da kambun zakarra na kwallon kafar kamaru. A gasar cin kofin Confederation Cup kuwa, a wani hali na ba sabon ba US Gendarmerie ta Nijar ta cancanci hayewa baya ga Salitas da kuma Diaraf . Sai dai a daya hannun an yi wa waje road da AS Maniema, inda Bloemfontein Celtic ta Afirka ta Kudu ta  fitar da kulob din Togo a bugun fanareti. Wasan farko na zagaye na gaba na Confederation club zai gudana ne a ranakun 22 da 23 na watan Disamba.
A Jamus, Bayern Leverkusen ta koma matsayi na biyu a teburin Bundesliga bayan nasarar doke Schalke 04 da ci 3-0 da ta yi a Gelsenkirchen a ranar Lahadi a wasan mako na goma. Ita dai Leverkusen wacce a yanzu take da maki 22 ta kusanci yawan maki ga Bayern Munich da ke saman teburi da maki 23 sakamakon kare jini biri jini da ta yi da RB Leipzig, inda aka tashi wasan ci 3-3 a ranar Asabar da ta gabata. Godiya ta tabbata ga Thomas Müller dan wasan gaba da ya sa Bayern farke kwallon da ake bin ta. Sai dai Müller ya bayyana takaicinsa dangane da mummunar dabi'a da kungiyarsu ta samu na bari a zuwa a zura musu kwallo kafin su rama wa kura aniyarta. Sauran sakamakon sun hada da nasarar Arminia Bielefeld a karo na biyu a bana a gaban Mainz 2-0, lamarin da ya ceto ta daga matsayin kurar baya da ta tsinci kanta a ciki. Yayin da Bremen ta doke Stuttgart da ci biyu da nema, a wasan 'yan gida daya kuwa, Hertha Berlin ta doke takwararta ta Union Berlin da ci biyu da nema. A nasu bangare kuwa Wolfsburg ta rike Cologne gam a gida da ci 2-2. Irin wannnan sakamakon na ci 2-2 aka samu tsakanin SC Freiburg da Borussia Mönchengladbach.

1. Bundesliga | SC Freiburg - Borussia Mönchengladbach
An yi canjaras a 2-2 a karawar da aka yi a tsakanin Freiburg da MönchengladbachHoto: Ronald Wittek/Getty Images


Sai dai yaya-karama Borussia Dortmund wacce ta sha duka a makon da ya gabata ba ta ji daddi ba a karshen mako inda ta yi kunnen doki ci 1-1 da Eintracht Frankfurt. Wannan dai ba ya rasa nasaba da rashin wasa na dodon ragarta Haaland sakamakon rauni da ya samu. Hasali ma shigo da dan wasa da ake yi wa lakabi da "yaro dan baiwa wato Yusufa moukoko bai tsinana wa Dortmund komai ba saboda bai yi nasarar zura kwallo ba tun bayan da ya fara bugawa a Bundesliga makonni ukun da suka gabata ba. Sai dai a Kamaru inda aka haifi Youssoufa Moukoko mai shekaru 16, masu sha'awar kwallo na kasar ke fatan ganin taurarin Moukoko ya ci gaba da haskawa.

Rennfahrer Mick Schumacher
Mick Schumacher yana shirin gadon mahaifinsa Micheal Schumacher a tseren motaHoto: SvenSimon/picture alliance

Mick Schumacher yana shirin gadon mahaifinsa Michael Schumacher na Jamus daga farkon shekara mai zuwa idan Allah ya kai mu. Za a iya tunawa dai mahaifin Mick wato Michael Schumacher wanda ya jima yana fama da rashin lafiya sakamakon hadarin da yayi, ya taba lashe kambun duniya na tseren motoci na F1 sau bakwai a tarihinsa. Shi ma dan nasa Mick ya nuna cewar, shi dan na gada ne a Lahadin da ta gabata, inda ya lashe kambun karamin aji na tseren motoci na Formula 2. A kakar wasa mai zuwa Mick Schumacher zai yi tseren F1 tare da kungiyar Haas ta kasar Amirka. Tuni ma Kimi Räikkönen, tsohon babban abokin adawar mahaifin Schumacher ya yi maraba da zuwan Mick. Mahifin Mick wato Michael Schumacher bai bayyana a bainar jama'a ba tun shekarar 2013 bayan wani mummunan hatsarin wasan gudun kankara wanda ya illata masa jijiyoyin jiki.