Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A Najeriya yunkurin sulhu a tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar mai ci yanzu Abdullahi Umar Ganduje ya bar baya da kura. Kan haka tashar DW ta yi hira da Kwankwaso.
Rundunar 'yansanda a jihar Kano, ta bayar da belin shahararriyar tauraruwar nan ta TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya. An dai kama Murja ne a jajiberin ranar da ta shirya bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Kano, ziyarar da aka shawarce shi ya dakatar da ita saboda fargabar abin da ya faru yayin makamanciyarta a jihar Katsina amma ya ce ba fashi.
A kokarin dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin wasu 'yan jam'iyyar APC kan batun sake fasalta takardar kudi ta naira a Najeriya, shugaban kasa ya gana da wasu gwamnoni.
Bayan faduwar kasuwannin CD da DvD, fina-finan Hausa sun koma YouTube da salon dogon zango wato "web series". Sai dai kasuwar ta zama iya ruwa fidda kai, ko kwalliya na biyan kudin sabulu?