1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi watsi da sukar tallafin farfado da tattalin arziki

Zulaiha Abubakar MNA
July 22, 2020

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi watsi da zargin da masu sukar lamirin samar da kudaden taimako da yaki da annobar corona suka yi bayan kammala taro.

https://p.dw.com/p/3ffvQ
EU-Sondergipfel zur Bewältigung der Corona-Wirtschaftskrise
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/EPA Pool/S. Lecocq

Masu sukar wannan kudiri na cewa shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun karya wasu dokoki da suka hada da na sauyin yanayi gabanin samun amincewar kasashe a taron da ya gudana a birnin Brussels na kasar Beljiyam.

Shugabar Hukumar ta EU, Ursula von der Leyen, ta kuma yi Allah wadai da furucin da 'yar fafutukar sauyin yanayi Greta Thunberg ta yi cewar kasafin kudin kungiyar bai yi la'akari da sauyin yanayi ba, game da zargin kasar Poland za ta mori kudaden kungiyar EU duk da ba ta goyi bayan kudirin kawo karshen gurbata muhalli daga yanzu zuwa shekara ta 2050 ba kuwa.

Shugabar hukumar Tarayyar Turan kuma tsohuwar ministar tsaron Jamus ta bayyana cewer a baya an karawa bangaren sauyin yanayi kudade daga kaso 25 zuwa kaso 35 cikin 100.

Bullar wannan cece-kuce na zuwa ne awanni kalilan bayan amincewar kungiyar kan batun kudaden taimakon kasashen Turai da suka fara fuskantar kalubalen tattalin arziki sakamkon annobar corona.