Kungiyar da ke sauya karantun allo a Nijar | Himma dai Matasa | DW | 06.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kungiyar da ke sauya karantun allo a Nijar

Kungiyar PAPEC da ke birnin Maradi na Nijar na fadi Ka tashi wajen aza makarantun allo kan sabuwar alkibla, inda take basu tallafin kayan aiki tare da horar da malamai.

Kungiya PAPEC ta wara aikinta na tallafi ga makarantun allo na Nijar tun a shekara ta 2006 da zumar kawo sauyi a tsarin koyarwa a cikinsu, wadanda galibinsu ke tafiya kara zube. Sannan kungiyra ta kawo sabon tsari na koyar da ajamin rubuta Haussa da harufa larabci.


Sama da makarantun allo 50 da ke cikin birnin Maradi ne suka samu
cin moriyar wanan tsari na PAPEC. Malam Manirou Madarasatul Hidaya ya ce an samu ci gaba matuka a wannan fanni. A fili yake cewa fafutukar wannan kungiya a kan makarantun allo ya sauya alkiblar tsarin karatunsu tare da kawo ci gaba ga fannin ilimi cikin kasar Nijar.