Kramp-Karrenbauer: Wajibi ne cika wa′adi | Labarai | DW | 12.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kramp-Karrenbauer: Wajibi ne cika wa'adi

Wadda ake zaton za ta gaji shugabar gwamnatin Jamus Angele Merkel, Annegret Kramp-Karrenbauer ta sanar da cewar ba zata nemi mukamin shugabar gwamnati kafin karshen wa'adin Merkel ya kare a shekara ta 2021 ba

A watan Disamban da ya gabata ne dai Kramp-Karrenbauer ta karbi ragamar shugabancin jam'iyyarsu ta CDU daga wajen Merkel, sai dai  shugabar gwamnatin ta ta ce zata cigaba da jagorantar gwamnatin hadar zuwa karshen wa'adin mulkinsu. 

Shugabar jam'iyyar ta nunar da cewar, an zabi Angela Merkel da 'yan majalisar Jamus din ne na tsawon wa'adin mulki, kuma al'umma na kyautata zaton zasu tafiyar da ayyukansu  da ke tattare da zaben har zuwa karshe.

A 'yan wannin nan kafofin yada labaru na Jamus sun yi ta yada jite-jite dangane da yiwuwar Merkel ta yi murabus daga mukaminta na jagorantar gwamnatin hadakar, kafin karshen wa'adin mulkinta a 2021.