Kotun ICC na bincike kan laifukan yaki a Najeriya | Siyasa | DW | 15.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kotun ICC na bincike kan laifukan yaki a Najeriya

Wata tawaga ta kotun kasa da kasa da ke sauraron kararraki kan laifkan yaki ta fara aikin gudanar da bincike kan keta hakkin bani Adama da ake zargin sojoji da 'yan Boko Haram da aikatawa a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Saurari sauti 02:56
Now live
mintuna 02:56

Rahoto kan binciken kotun ICC a Najeriya

Masu fafutukar kare hakkin bani Adama da kungiyoyin kasa da kasa sun shigar da kararraki gaban wannan kotun ta duniya bisa zargin aikata laifuka tsakanin bangarorin biyu da ke yaki a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya wato Sojojin Najeriya da kuma mayakan Boko Haram.

Ana zargin Sojojin da kame mutane da azabtar da su ko kuma cusasu cikin wuri da bai kamata bani Adama ya zauna ba. Kungiyoyin kare hakkin bani Adama sun kuma zargi Kungiyar Boko Haram da halaka fararen hula ba gaira ba dalili, lamarin da suke gani laifukan yaki ne da ya kamata a bincika tare da hukunta mai laifi.

Niederlande Den Haag Gerichtsvollzieherin Fatou Bensouda beim Fall Jean-Pierre Bemba

Babbar mai shigar da kara Fatou Bensouda ce ta tura da tawaga Najeriya


Minsitan shari’a na Najeriya Abubakar Malami wanda ya tabbatar da shirin kotun na fara bincike yayin da yake karbar tawagar kotun duniya da suka ka ziyarceshi a ofishinsa. Ya kuma kara da cewa akwai kararraki guda 8 kan Najeriya a gaban kotuna shida, inda ake zargin Kungiyar Boko Haram yayin da guda biyu kuma ake zargin Sojojin Najeriya.

Sai dai ya tabbatar da cewa Sojojin Najeriya sun gudanar da ayyukansu kan ka’ida tare da kare hakkin bani Adama a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya da ma dukkanin wuraren da suke aikin wanzar da zaman lafiya.

Kungiyoyi sun yi na'am da aniyar ICC na gudanar da bincike

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bani Adama a Najeriya suka karfafa goyon bayansu ga kotun da ta gudanar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi saboda zama darasi ga ‘yan baya.

Nigeria Boko Haram Terrorist

'Yan Boko Haram na cikin wadanda ake zargi da aikata ta'asa


Sai dai akwai masu ganin cewa ya kamata a yi taka-tsan-tsan da irin wadannan musamman a wannan lokaci da ake neman kawo karshen matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya. A cikin wata sanarwa da kakakin ministan shari’a na Najeriya Salihu Isah ya fitar ta nuna cewa tarayyar Najeriya za ta baiwa kotun duk wani goyon baya da ya kamata domin samun nasara gudanar da binciken domin ta san cewa ciki da gaskiya wuka ba ta hudashi.

Sauti da bidiyo akan labarin