ICC kotu ce da aka kafa domin hukunta manyan laifuka da suka danganci yaki da cin zarafin al'umma a duniya.
Kotun ICC na gudanar da aikinta ne a hedikwatarta da ke birnin The Hague na kasar Holland, ko da dai tana iya yin aikinta a wasu sassan duniya. ICC kan yi shari'un da kotuna na kasashe suka gaza yi. Kimanin kasashe 120 ne ke zaman mambobi yayin da wasu kasashe kamar Amirka da Sudan da Isra'ila ba su sanya hannu kan yarjejeniya ta amincewa da kotun ba.