Kotu ta halasta wa Najeriya kudaden da aka gano a Legas | Labarai | DW | 06.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta halasta wa Najeriya kudaden da aka gano a Legas

Wata babbar kotun tarayyar Najeriya ta umarci a maiyar wa gwamnatin kasar makudan kudaden da aka gano a wani gida da ke Legas, kudin da yawansu ya kai dalar Amirka miliyan 43 ba tare sanin hakikanin masu shi ba.

Mai shari'a Muslim Hassan da ya yanke hukuncin, ya ce kudaden ba a kai ga samun kwararan shaidu a kan wanda ya mallakesu da kuma abinda ake da niyar aikatawa da su ba. A watan Afrilu na wannan shekara ne hukumar yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta bankado kudaden a cikin wani gida da ke a Legas.

A baya dai hukumar leken asiri ta kasar NIA, ta yi ikirarin kudaden mallakan hukumar ce da niyar gudanar da wasu aiyuka a tsohuwar gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan. Bankado wannan badakalar ce ya sa gwamnati ta dakatar da shugaban hukumar leken asirin kasar don a gudanar da bincike.

Kawo yanzu dai ba a kai ga gabatar da rahoton bincike na kwamitin da aka nada su gudanar da bincike a kan shugaban hukumar da ya alakanta kansa da wadannan makudan kudade ba.