1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kotu ta aike da Shugaba Sarkozy gidan kaso

September 30, 2021

Wata kotu a Faransa ta samu tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da laifin aikata damfara. Hukuncin ya ce Sarkozy ya kashe kudaden da suka wuce kima a yakin neman zaben shugabancin kasa a shekara ta 2012.

https://p.dw.com/p/415kW
Nicolas Sarkozy
Hoto: picture-alliance/EPA/E. Lemaistre

Dokokin Faransa sun amincewa 'yan takarar shugabancin kasar su kashe kudin da ba su wuce Euro miliyan 22.5 ba, amma sai aka wayi gari Sarkozy ya kashe Euro miliyan 43 a yakin neman zaben nasa. Kotun ta ce Sarkozy ya san da wannan dokar amma, ya take sani, ya saba ka'ida. 


A sakamakon wannan laifi, kotun ta tura tsohon shugaban kasar gidan kaso na shekara daya. Sai dai kuma tsohon shugaban na Faransa ya ce zai daukaka kara.