Kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya | Siyasa | DW | 16.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya

A kokarin samo bakin zaren yakin ta'addanci a Najeriya da ke kwan gaba kwan baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaron kasar tare da maye gurbinsu da wasu sababbi.

Sai dai kuma har yanzu ana zaman jiran irin sababbin dubarun da sababbin jagororin sojojin za su bullo da su na yaki da masu tayar da kayar bayan. Ko shakka babu Najeriya da ke bukatar taimakon manyan kasashen duniya tana kuma bukatar sauyin fasalin yaki a bisa hanyar kaiwa ga gaci cikin matsalar da ke neman wucewa da sanin kowa.

Matsalar cin hanci da rashin isassunm kayan aiki da ma rashin kishin kasa na daga cikin dalilan da ake yi wa kallon ke kan gaba wajen gazawar sojan shawo kan matsalar bayan share shekara da shekaru.

DW.COM