Buhari ya nada sabbin jagororin tsaro | Siyasa | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya nada sabbin jagororin tsaro

Wannan mataki na shugaba Muhammadu Buhari na zuwa adaidai lokacin da manyan jami'an tsaron kasar suka shiga wata tattaunawa kan lamuran tsaro.

Niger Buhari Issoufou

Shugaba Muhammadu Buhari

Dama dai karuwar kai hare-hare na kunar bakin wake da ake fuskanta ne suka mamaye taron da sojojin kan yi, da nufin laluben mafita daga matsalar. Rundunar sojan Najeriyar ta bayyana cewa ya zuwa yanzu ta karbe daukacin garuruwan da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka kame a lokutan baya, inda kawai ya rage a hannunsu shi ne wani sashi na gandun dajin Sambisa.

To ko wadanne sabbin dubaru suke shirin dauka a yanzu. Lieutenant General Kenneth Minimah shi ne tsohon babban hafsan sojan Najeriyar da aka yiwa ritaya jim kadan bayan fara taron koli na sojojin Najeriya.

Nigeria Poster von Präsident Mohammadu Buhari vor Militär

Jami'an tsaro a Najeriya

Samun bayanan sirri

‘'Yace dabarar da nike tunanin dauka a kan wannan ba abu ne da zamu bayyanawa jama'a a fili ba, amma dai mun samu bayanai na sirri a kan kudurin da masu kai hare-hare suke da shi da ma shirinsu, saboda haka ba zamu zauna mu rungume hannu ba, zamu dauki mataki. Kuma saboda wannan sauyi da suka yi ai mun samu kwato daukacin wuraren da suka kame,yanzu muna cikin gandun dajin Sambisa mun shiga lungunansa domin tabbatar da cewa mun 'yantar da wannan wurin''.

Batun 'yantar da gandun dajin Sambisa da ma daukacin wuraren da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram ta kame dai muhimmin batu ne ga sojojin da ke jinjinawa kansu a matsayin samun nasara, to sai dai ga ‘yan Najeriya da ke dandana azabar matsalar karuwar kai hare-hare na bayyana da fa sauran jan aiki a gaba, amma ga kanal Sani Usman ya ce akwai dalilin karuwar kai hare-haren kuma suna daukar mataki:

Nigeria Boko Haram Terrorist

Mayakan Boko Haram

Burbushin mayaka

"Mutane ne da suke zaune sun kame garuruwa da wurare da dama, yanzu galibi an kashe su kuma sauran duk sun kaura, kuma wadanan sansanoni duk babu in dai ba gandun dajin Sambisa ba. To akwai dan burbushinsu da su ne suke son inda za su yi yakin sari ka noke don su nuna cewa suna nan, kuma yadda aka kakabe sauran suma haka za'a kakkabe su".

Sauti da bidiyo akan labarin