Kokarin magance matsalar kwari a yammacin Afirka | Siyasa | DW | 19.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin magance matsalar kwari a yammacin Afirka

Masana harkokin noma da kiwo na kasashen Liptako Gourma da suka hada da Mali, Burkina Faso, da Nijar sun gudanar da taron koli a wani mataki na shayo kan matsalar cije-cije da ke lalata amfanin gona.

Karo na takwas kenan da hukumomin kasashen uku na Liptako Gourma masu fafutukar bunkasa noma da kiwo ke halarta irin wannan zama da zimmar dakushe matsalolin kwari masu lalata dimbin amfanin da manoman kasashen ke nomawa da kuma galibi rashin daukar matakai a kansu ke haifar da illoli da ma barazanar jefa kasashen cikin wani hali na karancin abinci.

Burkina Faso Landwirtschaft Ouagadougou Seydina Oumar Traor (DW/P. Hille)

Seydina Oumar Traore masanin harkokin noma a Burkina Faso.

Taron dai na zuwa ne biyo bayan wani rahoton bincike da hukumar CILSS ta wallafa mai kula da noma da yaki da hamada a kasashen Sahel inda ta ambaci fargabar bulluwar Farar dango da kuma kwarin da ke barazana ga amfanin gonaki a wannan shekarar a kasashen Sahel ciki har da kasashen uku na Liptako Gourma.

Kwararrun  daga kasashen na Mali, Burkina Faso, da Nijar da ke halartar taron, na bita ne kan halin da kasashen suka kasance a shekarun 2016 da 2017 tare da tsaida tsarin da kasashen za su yi amfani da shi wajen yin fito na fito da cututkan masu kawo nakasu harkokin noma da kiwo. Kwararrun za su duba ingantattun hanyoyi don samun tallafin kasa da kasa duba domin fuskantar lamarin a kasashen uku na Liptako Gourma suke a ciki yanzu.

Symbolbild Afrika Anbau Wasser (Issouf Sanogo/AFP/GettyImages)

Wani manomi kayan lambu a kauyen Yamai a Jamhuriyar NijarYayin wani taron kolin shugabannin kasashen yankin ne dai aka yanke hukumcin fadada ayyukan kungiyar daga dan karamin yankin da ke hada iyakokin kasashen ya zuwa daukacin fadin kasashen domin magance matsalolin tsaro da bunkasa ayyukan noma da kiwo da kuma harkokin kasuwanci.

Sauti da bidiyo akan labarin