Kokarin magance matsalar karancin kaji a Nijar | Himma dai Matasa | DW | 20.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kokarin magance matsalar karancin kaji a Nijar

Wani matashi ya buda cibiyar kiwon kaji da sayarwa wani kauye mai suna Bartcawel da ke a karamar hukumar Hamdallaye mai nisan km 25 da birnin Yamai.


Kauyen na Bartcawel da ke cikin karamar hukumar Hamadallaye mai tazarar kilo mita 25 daga Yamai kenan inda matashin dan shekaru 32 mai suna Mourtala Himadou ya zaba don girka wannan masanaanta ta kiyo da sarafa kaji, a nan wani shinge ne hadi da wasu tarin injina a yayin da wasu tarin matasa ke tsaye don binciken lafiyar kajin da ake shirin shigar wa a mayanka bayan dauko su daga wurin kiyo, a ya yin da a gefe daya, wasu manyan dakuna ne biyu ake kiyon kajin a cikin su. Malam Abdoulaye Mounkaila shi ne babban jamiin da ke kula da masanaantar:


"Wannan dakunan ko wane daya yana daukan kaji dubu 27 kuma tun suna kankana ake kawosu, sannan mu yi kiwon su har kwanaki 45 zuwa 50 kafin mu kai su a mayanka masanaantar dai na a matsayin irin ta ta farko a kasar ta Nijer inda akalla maaikata fiye da 100, kama daga masu kiyon kaji har izuwa masu aikin yanka kajin ke aiki a ko wace rana. Kamfanin na da kayayakin zamani wanda akalla yake yanka kaji 1,500 ko wace awa:

"Idan aka yanke su, sai su shiga inda ke da ruwan zafi daga nan sai wurin da ake fige su nan kuma sai su wuce wurin da ake fede su sai wurin da ake yanke kawunansu da kafafuwa sai kuwa su isa inda ake wankewa kafin su iso a nan inda muke."


Wannan masanaantar za ta taimaka wajan rage korafin cin kaji masu sanyi da ke shigowa kasar daga kasashen waje. Tuni dai masana ke ganin cewa idan har gwamnati ta taimaka, to ba shakka za a ciyo kan matsalar karamcin cimaka inji Farfesa Djibo Hamani na jamiar birnin Yamai da na tarar da shi ya zo sayen kajin da matashin ke samarwa:


" Idan aka basu taimako kudaden da za a samu a cikin kasa za su tsaya kuma suna daukar maaikata kenan suna taimakon mutane da yawa."


Sai dai wata matsalar ita ce kajin da masanaantar ke sayarwa na fuskantar kalubalen farashi inda ake sayar da su akan jika biyu da tamma 750 na CFA. a ya yin da kajin da ake fitowa da su masu sanyi daga waje ake sayarwa akan jika biyu kawai, amma kuma duk da haka kajin na samun karbuwa. Sai dai duk da wadannan nasarorin da ake gani kan wannan masana'anta da matashin ya girka, wani babban kalubale da maaikatar ke fuskanta shi ne na karamcin wutar lantarki da kuma tsabagen kudaden haraji, abubuwan da matashin ya ce zai iya kai ka karya manufarsa ta yaki da karamcin cimaka da matsalar shigowa da kaji daga waje uwa uba samarwa matasa aikin yi.