Kokarin karbe iko da Deir Ezzor a Siriya | Labarai | DW | 11.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin karbe iko da Deir Ezzor a Siriya

Hukumomin Siriya sun aike da karin dakaru domin dafa wa takwarorinsu a kokarin da suke yi na karbe iko da birnin nan Deir Ezzor da ke karkashin ikon mayakan kungiyar nan ta IS.

Masu aiko da rahotanni sun ce tuni aka aike da motoci da jiragen yaki da sauran kayan aiki gabannin dannawar da sojojin na Siriya za su yi don maido da birnin karkashin ikon gwamnati. Tuni ma wadanda ke sanya idanu a kan abubuwan da ka je su komo a birnin suka ce jiragen yakin Siriya da na Rasha sun kara zafafa kai hare-hare ta sama a ciki da waje birnin wanda 'yan IS din ke rike da shi tun shekarar 2014. Siriya dai na daga cikin kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya da 'yan kungiyar IS suka shiga da nufin mallake wasu sassa don girka daular Islama.