Kokarin EU na kawar da cutar Ebola | Labarai | DW | 23.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin EU na kawar da cutar Ebola

Kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce ya zuwa yanzu ta sanya kimanin euro miliyan ashirin da hudu da rabi don neman magunguna da ma rigakafin cutar nan ta Ebola.

EU din dai ta ce ta dauki wannan matakin ne domin gaggauta shawo kan annobar ta Ebola, inda ta kara da cewar ta na aiki kafada da kafada da wani kamfani da ke yin magunguna domin kaiwa ga samun magununan rigakafin cutar cikin gaggawa.

Baya ga wannan kuma, kasashen da ke cikin kungiyar ta EU din za su bada gudunmawa ga al'ummar da wannan ibtila'i ya shafa kana kungiyar za ta bada gudumawar jami'an kiwon lafiya duka dai a yunkurinta na ganin an dakile bazuwar cutar.