1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gargadi Isra'ila a kan kogin Jodan

June 10, 2020

A wata ziyara da ya kai ta farko a wata kasar waje tun da annobar corona ta ta'azzara, Ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas ya soki lamirin Isra'ila na yunkurin mamaye yankin yamma da kogin Jodan.

https://p.dw.com/p/3dbcf
Israel Jerusalem | Heiko Maas und Benjamin Netanjahu
Hoto: picture-alliance/photothek/F. Gaertner

A ziyararsa ta farko da ya kai a wata kasar ketare tun bayan bullar cutar corona, Heiko Maas ya ja kunnen Isra'ila da kada ta kuskura ta aiwatar da kudurinta na mamaye yankin nan na yamma da kogin Jodan wanda a cewarsa hakan wani kokari ne na yi wa  dokokin kasa da kasa karan tsaye.

Mr Maas din ya fito karara ya soki lamirin na Isra'ila wanda ya ce Jamus da kungiyar Tarayyar Turai ba su amince da abin da Isra'ilar ke kokarin aikatawa ba.

Yunkurin dai na Isra'lar na zuwa ne a daidai lokacin da Jamus ke shirye-shiryen karbar jagorancin kungiyar Tarayyar Turan na karba-karba da kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya nan da 1 ga watan Yuli mai kamawa, wanda wannan ranar ce Isra'ila ta tsaida domin kwace yankin.