Kiran shugabannin addini kan Boko Haram | Siyasa | DW | 08.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kiran shugabannin addini kan Boko Haram

Sarkin Musulmi a Najeriya Mohammad Abubakar Sa'ad III ya gana da malaman addinin Musulunci da na Kirista inda suka bukaci gwamnatin kasar ta sulhunta da kungiyar Boko Haram

Malaman addinai a Tarayyar Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar da ta tattauna da 'yan kungiyarBoko Haram, wadda aka fi sani da Boko haram, dan kawo karshen tayar da zaune tsaye a cikin kasar

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya kenan Alhaji Mohammad Abubakar Sa'ad kenan ke yin kira ga gwamnatin kasar, dan ganin cewa ta koma kan teburin tattaunawa da dukkanin masu tayar da kayar baya a cikin kasar, da zumar kawo karshen zubar da jinin bayin Allah, da garkuwa da 'yan mata da dargwajewar bama-bamai a kasuwanni da wuraren ibada, da kai farmaki a makarantu don samun dorewar zaman lafiya a cikin kasar.

Sarkin dai ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da wata tawaga ta limaman coci-coci suka kai masa ziyara tare da yin liyafar bude baki don karfafa dankwan zumunci, inda ya nunar da cewa yawancin tashe-tashen hankula da rigingimun da ke tayar da hankalin 'yan kasar, ' yan siyasar Nigeria ke haddasa su, wadanda suka hada da matsalolin rashin zaman lafiya wanda ke addabar wannan kasar, kuma a cewarsa duk ana haddasa wadannan fituttune ne don zaben shekara ta 2015 da ke gabatowa, a saboda haka ya gargadi 'yan siyasa da su ji tsoron Allah

Wannan tawaga ta Kiristoci dai na anfani da wannan wata na azumin watan Ramadan don kara karfafa kyakkyawar dangartaka da fahimtar juna da zumar dakile ci-gaban tashe-tashen hankula tsakanin Musulmai da Kirista a cewar Sheikh Ibrahim Yakub Alzazzaki, shugaban daukacin 'yan Shi'a a Nigeria yayin da suka kawo masa tasa ziyara

"Ana amfani da wasu hanyoyin ne na haddasa rudani da tashe-tashen hankula, kuma muna ganin cewa lokaci ya yi da dukkanin 'yan Nigeria za su hada kai wuri daya, don magance ci gaban rigin-gimun da suka hada da na addini, kabila da siyasa da ke shafar tattali arzikin kasa"

A yanzu haka dai bukatar komawa kan teburin tattaunawa dan dakile karuwar tashe-tashen hankula da dagwajewar makamai, ita ce dai babban burin da kungiyoyin kare hakkin bil adama da na fararen hula na cikin gida da na kasashen ketare yi ke fatan ganin an samu.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin