Kimanin sojojin Najeriya 500 sun tsere zuwa Kamaru | Labarai | DW | 25.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kimanin sojojin Najeriya 500 sun tsere zuwa Kamaru

Da ma dai sojojin Najeriya da aka tura su yaƙi Boko Haram sun sha ƙorafin cewar ba su da isassun kayan aiki wanda hakan ya sa suke zin asara mai yawa.

Kusan sojoji 500 na Tarayyar Najeriya sun gudu zuwa Kamaru bayan sun fafata da Ƙungiyar Boko Haram. Kakakin ma'aikatar tsaron Kamaru Didier Badjeck ya faɗa wa kamfanin dillancin labarun Jamus na DPA cewar yawan sojojin da suka tsere ya kai 484, kuma an tura su yaƙi ne da Boko Haram a garin Gamboru Ngala da yanzu haka aka ce yana hannun kungiyar ta masu kaifin kishin Islama. An kwance ɗamarun sojojin kuma yanzu haka an tsugunar da su a wasu makarantu da ke Maroua, babban birnin jihar Arewa mai Nisa, wanda kuma ke tazarar kilomita 80 da iyakar Najeriya. A martanin da ta yi, kakakin ya ce Kamaru ta ƙara yawan sojojinta a wannan yanki. Tun a cikin watan Mayu Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ƙaddamar da yaƙi a kan Boko Haram bayan da ƙungiyar ta fara yin kutse cikin Kamaru.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahmane Hassane