Biya dan siyasa ne a Jamhuriyar Kamaru kuma ya dare kan kujerar shugabancin kasar a shekarar 1983.
Gabannin zamansa shugaban kasa, Biya ya rike mukamin minista da kuma na firaminista a gwamnatin Ahmadu Ahidjo wanda ya yi murabus a farkon shekarun 1980. Ya zuwa yanzu Biya na daga ckin shugabannin Afirka da suka fi jimawa kan gadon mulki.