Kiki-kaka a zaben kasar Kenya | Siyasa | DW | 19.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kiki-kaka a zaben kasar Kenya

Hukumar zaben kasar Kenya ta ce duk da shiri da ta yi na gudanar da zabe zagaye na biyu yana da matukar wuya a bada tabbacin gudanar da tsaftataccen zabe a kasar, a dai lokacin da jagoran adawa da magoya bayansa ke bore.

Shugaban hukumar zaben kasar Kenya ya bayyana cewa duk da cikakken shiri da hukumar zabe ta yi na gudanar da zabe zagaye na biyu, yana da matukar wuya a bada tabbacin gudanar da tsaftataccen zabe a kasar, hakan na zuwa ne baynda m,adugun yan adawar kasar yayi kira ga mafoya bayan sa da su fito zanga-zanga a ranar da aka shirya don gudanar da zaben. Shugaban hukumar zaben na kasar Kenya Wafula Chebukati ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a ranar laraba inda ya bayyana cewa rarrabuwar kai tsakanin kwamishinonin hukumar zaben da ma katsalandar da hukumar ke fuskanta daga 'yan siyasa, abu ne mai wuya a gudanar sahihin zabe a kasar a ranar 26 ga watan Oktoba.

Kenia - Wahlen - Vorsitzender des Independence Electoral and Boundaries Commission Wafula Chebukati bei Pressekonferenz (picture-alliance/AP Photo/S. A. Azim)

Shugaban hukumar zaben Kenya

Shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa duk da kokari da ya yi na gudanar da cikakken shiri da hada kan ma'aikatan hukumar zaben abu ya ci tira. ''Ya ce na yim kokarin samar da muhimman sauye-sauye, amma galibin jami'an hukumar zaben ba su amince da bukatu da na gabatar musu ba. Don haka da wuya ne a samu sahihin zabe''

Ajiye aiki da wata babbar kwamishiniya a hukumar ta yi, ya tabbatar da dalilai da shugaban  hukumar zaben kasar  ya bayar. Ita dai Roselyn Akombe ta ajiye aiki ne a wata sanarwa da fitar daga birnin New york na kasar Amurka tana mai bada dalilan cewar ba abu ne mai yiwuwa ba a samu zabe mai tsafta ganin irin matsalolin da suka yi wa hukumar zaben dabaibayi.

Kenia nach der Annulierung der Präsidentenwahl | Uhuru Kenyatta (Getty Images/AFP/T. Karumba)

Shugaba Uhuru Kenyatta

A nashi bangaren shugaban kasar ta Kenya Uhuru kenyatta nuna kwarin gwiwa ya yi kan gudanar da zaben inda ya ci gaba da yakin neman zabe. Ya kuma kira malaman addinai na kasar a wani taron gaggawa inda ya bukace su da su dukufa wajen yin adu'o'in zaman lafiya a kasar.

''Ya ce mataki na farko da zan kira a halin yanzu shine dukufa cikin adu'a da kuma sasantawa a karshen wannan makon, bayan tattaunawa da shugabannin addini ina kira ga daukacin alumma kenya da su gudanar da adu'oi wa kasarsu,

 A yayin da shugaba Kenyatta ke nuna kwarin gwiwar gudanar da zagaye na biyu na zaben, shi kuwa madugun 'yan adawa Raila Odinga bayan sanar da janye shiga takarar zaben, ya yi kira ga magoya bayansa ne da su fito zanga-zanga a ranar 26 wacce a ka sanya dan gudanar da zaben.  Tuni dai wasu al'umar kasar ciki harda masu sharhi kan al'amuran yau da kullum ke bayyana cewa a yanzu ya kamata dukkan 'yan takara su zauna a teburin sulhu dan samar da mafita.

DW.COM