Janyewar Odinga shiga zabe na haifar da fargaba | BATUTUWA | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Janyewar Odinga shiga zabe na haifar da fargaba

Al'ummar kasar Kenya na ci gaba da mayar da martani bayan da madugun 'yan adawa Raila Odinga, ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a zaben shugaban kasa da za a sake shiga a ranar 26 ga watan Oktoba ba.

Madugun 'yan adawar kasar Kenya Raila Odinga, ya sake jaddada bukatarsa tun da fari, na ganin an sauya tsarin zaben da ma sauya wasu jami'ai a hukumar zaben kasar, wadanda ya zarga da hannu a murde sakamakon zaben watan Agusta da kotun kolin Kenya ta soke, inda ya ce:

"Tsarin kundin mulkin demokradiya bai kamata a rika ma muhawara ba, kan yadda za a samu zabe mara almundahna a cikinsa ko bin umarni na kotu ko amfani da madafun iko a yaudari al'umma, sai dai hukumar zaben Kenya IEBC ta ki mutunta umarnin kotu a samar da sauyi cikin masu gudanar da zaben, ta yadda za a samu sakamakon zabe wanda ba almundahna a cikinsa."

A cewar Odinga, tanadi ko shiri da hukumar zaben ta yi a wannan karo sai yafi muni a kan zaben da aka tsara a watan Agusta, wacce kotu ta rushe sakamakonsa.

Kenia Wahl Annullierung Uhuru Kenyatta (Reuters/T. Mukoya)

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta

Tuni dai Shugaba Uhuru Kenyatta ya mayar wa da madugun adawar martani, yace:

"Abokina na ji ka janye daga takara bayan lokaci mai tsawo muna shiri tare da kashe kudin Kenya, sama da miliyan dubu goma na Shillings don shirin komawa rumfunan zabe, kudin da ya kamata a yi amfani da su wajen gina titunan mota da asibitoci, mun yi amfani da su wajen shirya zaben da ka kira. Amma yanzu ka ce ba za ka shiga ba, wannan ya zama adalici kenan?"

'Yan siyasa da ke kusa da Raila Odinga sun nemi jagoran adawan da ya ci gaba da jagorantar zanga-zangar lumana a fadin kasar, yayin da bangaren shugaba Kenyatta, ya ce za a yi zaben kamar yadda kotu ta bada umarni. Wannan ya sa wata a cikin mazauna birnin Nairobi ke bayyana ra'ayin ta da cewa:

"Ni bani da wata fargaba ta tashin hankali, ina ga al'ummar Kenya sun samu ci gaba, suna dai iya yin wasu tambayoyi amma al'ummar Kenya a yau burinsu shi ne zaman lafiya"

Shi kuwa a nasa ra'ayin David Keya, yana fargabar irin tashin hankali da kasar ka iya fadawa a ciki.

"Akwai alamu na samun hargitsin siyasa muddin aka rantsar da Uhuru Kenyatta: Tuni mutane ke dari-dari da fargaba saboda rikici ne na siyasa da aka kafa ginshikinsa akan banbancin kabila, abin da kuma zai hana ci gaba da rashin zaman lafiyar demokradiya."

Babbar kotun kasar dai na shirin ba wa dantakarar Kenya Ekuru Aukot ya shiga a fafata da da shi a zaben. A bangare guda kuma 'yan majalisa sun amince da tsarin cewa duk dan takarar da ya janye a yanayi na sake zabe, to wanda za a fafata da shi ya ci ba hammayya, to ko wannan ya shafi Odinga da Kenyatta. Bobby Mkangi kwararre ne kan kundin tsarin mulki a Kenya.

"Idan da ace janyewar ya yi ta bayan kudirin ya zama doka, to da abin ya shafi Odinga, amma a yanzu sai ma shugaban kasa ya sa hannu kafin ya zama doka.

Magoya bayan Odinga sun gudanar da zanga-zanga, wacce tuni aka fara karo da jami'an tsaro, a bin da ya haifar da fargabar rikicin siyasa da irinsa a shekarar 2007, wanda ya yi sanadin rayukan mutane 1,200.

Sauti da bidiyo akan labarin