′Yan kasar Kenya na fama da dambarwar siyasa | Siyasa | DW | 12.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan kasar Kenya na fama da dambarwar siyasa

Tun bayan da kotun tsarin mulkin kasar Kenya ta soke zaben shugaban kasar dambarwar siyasa ke daukan sabon salo.

Kenia Präsidentschaftswahl Proteste in Nairobi (Reuters/T. Mukoya)

Rikicin bayan zabe a kasar Kenya

Al'amuran siyasar kasar Kenya dai sun dauki wani sabon salo, tun bayan da dan takarar Raila Odinga da ya kalubalanci shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyata ya sanar da aniyarsa ta kin zuwa zaben na ranar 26 ga wannan wata na Octoba ta sabili da abun da ya kira rashin daukan matakan shirya sahihin zabe. Kuma Odinga ya ce kin halaratasa zaben ya na nufin soke zaben ga baki dayansa. Hakan kuma ta sanya magoya bayansa da dama suka fifo a ranar Laraba a titunan biranen kasar domin goya masa baya abun da ya kai su dauki ba dadi da jami'an tsaro na 'yan sanda. Ra'a yoyi dai sun bambanta tsakanin 'yan kasar ta Kenya kan halin siyasar da kasar ta samu kanta ciki.

Kasar ta kenya dai na daga cikin kasashen da ake fuskantar rikici na bayan zabe. A wannan karo ma dai tun bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta soke zaben shugaban kasar da ya gudana na ran takwas ga watan Augusta ake ana ci gaba da fuskantar rikicin siyasa iri-iri, inda yayin da dan takara Raila Odinga ke neman da a koma ga sabon tsari na sabon, shi kuma shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya ce ala tilas sai an yi zabe na ran 26 ga watan Octoba.

Sai dai mataki na baya-bayan nan da hukumar zaben kasar ta Kenya ta dauka, shi na ta tabbatar da ranar 26 ga watan Octoba a matsayin ranar zaben shugaban kasar, amma kuma tare da bai wa sauran 'yan takara da suka fafata a zagaye na farko damar sake shiga zaben.

DW.COM